IQNA

Kotu Ta Saki Wasu ‘Yan Uwa Musulmi Da Ake Tsare Da Su A Kaduna

23:00 - February 22, 2020
Lambar Labari: 3484549
Tehran – (IQNA) babbar kotun koli da ke Kaduna najeriya ta saki ‘yan uwa musulmi 91 da ake tsare da su tsawon fiye da shekaru hudu.

Rahotanni daga Najeriya sun ce bayan zaman da kotun ta gudanar, alkalin ya kotun ya bayar da umarnin sakin mutanen wadanda dukkaninsu ‘ya’yan Harka Islamiyya ne, wadanda aka kama su tun bayan harin da sojoji suka kai Zaria.

Bayanin ya ce alkalin bai gamsu da dukkanin tuhumce-tuhumcen da ake yi kan mutanen ba, da hakan ya hada da kashe soja guda, wannan kuwa ya zo bayan kasa gabatar da wasu kwararan dalilai da za su iya tabbatar da abin da ake tuhumar mutanen.

Tun  a karshe shekara ta 2015 ne dai sojojin Najeriya suka kaddamar da farmaki kan wurin taro na na Harkar Musulunci da ak afi sani da Husainiyar Baqiyatullah a Zaria, bisa hujjar cewa magoya bayan harkar muslunci sun tsare hanyar wucewar babban hafsan sojojin kasa.

Sojojin sun kashe mutane a wurin, kafin daga bisani suka kaddamar da farmaki kan gidan Sheikh zakzaky, inda suka kashe mutane masu tarin yawa, inda gwamnatin Kaduna ta tabbatar da cewa ta bizne gawawwakin mutane dari uku da arba’in da bakawai daga cikin wadanda aka kashe, yayin da majiyoyin Harka Ismiyya ke cewa an kashe mutane fiye da dubu daya a harin.

3880663

 

 

 

 

captcha