IQNA

Kotun Tarayya Ta Yi Watsi Da Karar Sheikh Ibrahim Zakzaky

23:40 - July 07, 2017
Lambar Labari: 3481677
Bangaren kasa da kasa, kotun tarayya da ke Kaduna a rewacin najeriya ta yi watsi da karar da sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a kan kisan gillar Zaria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni daga tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa alkalin babbar kotun tarayya a Kaduna ya sanar da yin watsi da karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a kan rundunar sojin kasar da kuma babban hafsan sojoji a kan kisan gillar Zaria.

Alkalin kotun dai ya bayyana cewa, bayan vin dukaknina bubuwan da aka gabatar a cikin karar, ya kai ga sakamakon cewa ba zai yiwu kotunsa ta saurari karar ba, bisa hujjar cewa an shigar da wasu kararrakin irin wannan a wasu kotunan a Abuja.

Sai dai anasa bangaren lauyan da ke kare sheikh Ibrahim zakzaky ya bayyana cewa, abubuwan da aka shigar da kara akansu a gaban wannan kotu, babu wata kotu ta daban da aka shigar da kara agabanta a kan wannan batu.

Ya ce kotun Abuja an shigar da kara ne a kan tsare sheikh Zakzaky da mai dakinsa ne ba tare da wani dalili ba, a kan aka nana bukatar kotu ta bayar da umarni a jami'an hukumar tsaro ta SSS su sake su, kuma kotu ta bayar da umarnin yin hakan ga gwamnatin tarayya wanda har yanzu ba a aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar ba.

Amma batun shari'ar kotun tarayya a Kaduna ana maganar kisan gilla ne da aka yi a Zaria da kai hari a kan gidan malam Zakzaky tare da kashe iyalansa da kuma rusa masa gida, wanda ake karar sojoji da babban hafsansu na kasa a kan wannan laifi da aka shigar da kara akansa.

A ranar 14 ga watan Disamban shekara ta 2015 ce dai jami'an sojin Najeriya suka kaddamar da haria kan gidan Sheikh Zakzaky tare da kasha daruruwan mabiyansa, bisa zargin wasu daga cikin mabiyansa da tarewa babban hafsan hafsoshin sojin najeriya hanya a lokacin da yake wucewa.

3616165


captcha