Jagororin msuulmin sun sanya hannu ne kan budaddiyar wasikar zuwa ga sabon shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, suna masu jawo hankalinsa da ya dauki matakan da suka dace a lokacin shugabancinsa wajen ada kan dukkanin al'ummar Amurka duk kuwa da banbancin akidu da addinansu.
Kamar yadda kuma suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda kyamar msuulmi ta karu matuka a kasar tun bayan da aka sanar da cewa ya lashe zaben shugaban kasar, sakamakon irin kalaman da ya rika furtawa alokacin yakin neman zaben na cin zarafi a kan musulmi, wanda ya bar mummann tasiri.
Kamar yadda kuma wasikar ta kirayi dukkanin al'ummar Amurka da su zama masu kiyaye kaidoji da dokokin kasa, domin kuwa dokar kasar ba yarje wa wani ya ci zarafin wani ba saboda akidarsa ko addininsa ba.