Sai dai a nata a bangaren kungiyar yan wasar Judo ta kasa da kasa ta yi barazanar horo ga dan wasan kasar Masar wanda ya ki bawa abokin karawarsa daga haramtacciyar kasar Isra'ela hannua gasar Olympic wanda ake gudanarwa a halin yanzu a kasar Brazil.
Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran a Rio de Jenero ta nakalto Nicolar Misnar kakakin kungiyar yana fadar haka a jiya jumma'a bayan kammala wasantsakanin yan kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa Islam Shihabi dan wasan judo daga kasar Masar a wasan Judo na masu nauyin kilo dari, yaki bawa dan wasan HKI kuma abokin karawansa hannu kamar yadda aka saba a wasar don bayyana kiyayyarsa ga HKI. A karshen wasan dai bayahuden ya sami nasara a kan Islam Shihabi.