IQNA - Wata tsohuwa Bafalasdiniya wadda ta yi shekaru 70 dtana yin sallah da addu'o'i a Masallacin Al-Aqsa ta samu yabo daga masu amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo kuma ana kiranta da abin koyi.
IQNA - Hukumar Ba da Agaji da Samar da Aikin yi ga Falasdinu ‘Yan Gudun Hijira (UNRWA) ta sanar da cewa, sama da malamai 8,000 a shirye suke don taimakawa yara su koma karatu da kuma ci gaba da ayyukan makaranta a zirin Gaza.
IQNA - An gudanar da bikin karrama zababbun jami'o'i da kwamitin alkalai da suka halarci gasar kur'ani ta jami'ar kasa da kasa ta "Al-Nour" a jami'ar Al-Ameed da ke kasar Iraki.
IQNA - Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana a cikin sakonsa cewa gwamnatin sahyoniyawan da Amurka ba za su iya karya lagon Hizbullah ba.
IQNA - Kusan mutane 30 ne suka gurfana a gaban wata kotun birnin Landan karkashin dokokin yaki da ta'addanci, kuma ana tuhumar su da laifin goyon bayan wata kungiyar da ke goyon bayan Falasdinu.
IQNA - Babban Mufti na masarautar Oman Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya yi kakkausar suka ga sojojin hayar Isra'ila da ke mamaya a zirin Gaza tare da yin kira ga masu adawa da kada su yi watsi da kowa daga cikinsu.
IQNA - Mukaddashin Sakatare Janar na Sakatariyar Awkawa ta Kuwaiti ya sanar da gudanar da gasar karatun kur'ani da hardar kur'ani ta kasa karo na 28 a kasar.