Kamfanin dillancin labaran Bernama ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da gasar karatun kur’ani da haddar kur’ani ta kasa da kasa ta Malaysia karo na 63 a cibiyar kasuwancin duniya ta Kuala Lumpur (WTCKL). An fara wannan gasa a hukumance da yammacin ranar 28 ga watan Agusta a dakin taro na Merdeka dake cibiyar kasuwanci ta duniya bayan bude taron tare da halartar manyan jami'an kasar Malaysia kuma aka kammala a ranar 2 ga watan Satumba tare da gabatar da wadanda suka yi nasara.
A bangaren karatun maza, Mohammad Qayim Nizar Sarimi, mai karatu dan kasar Malaysia, ya samu matsayi na farko da kashi 94.96 na maki.
A matsayi na biyu ya samu Ali Reza Bijani daga Iran da maki 93.30% sannan Mohammad Zul Hafez Awang Tangah daga Brunei ya samu matsayi na uku da maki 90.38%.
Sara Balmamoun ‘yar kasar Moroko mai karatu ce ta samu matsayi na farko a bangaren karatun mata da maki 93.05, Roza Sufyan Noor daga Indonesia (92.21%) sai Sabahe Batu Salek daga Philippines (91.50%).
A fagen haddar kur'ani mai tsarki ga maza Omar Toure daga Guinea ne ya zo na daya da maki 98.63, sai kuma Mamoun Ahmed daga Yemen da kashi 97.38% da Ali Atiyeh na Chadi da kashi 97.07% a matsayi na gaba.
Tibani Shima Anfal ta Aljeriya ta samu matsayi na daya a cikin mata a wajen haddar kur’ani mai tsarki da maki 96.32%, sai Nadi Sinabo Najoom daga Senegal (95.25%) sai Sidi Al-Mukhtar Khadijito daga Mauritania (94.19%).
Muhammad Qayim makaho dan kasar Malaysia wanda ya yi nasara a matsayi na daya, ya ce: Na gode wa Allah da kokarinsa na tsawon shekaru 16 na koyon fasahar karatun kur’ani mai tsarki a cikin harshen Braille a karshe ya samu nasara a wannan gasar.