IQNA

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da hari kan ofishin raya al'adu na Saudiyya a Sudan

17:01 - May 04, 2023
Lambar Labari: 3489088
Tehran (IQNA) Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta mayar da martani inda ta fitar da sanarwa game da harin da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai kan ofishin raya al'adu na Saudiyya a birnin Khartoum tare da yin Allah wadai da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Rasd News ya habarta cewa, a cikin wata sanarwa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar, ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin raya al'adu na kasar Saudiyya a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta jaddada bukatar kawo karshen tashe-tashen hankula, da mutunta alfarmar gine-gine da cibiyoyin diflomasiyya, da kuma tabbatar da tsaron da ya dace ga jami'an diflomasiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta sanar a baya a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, wasu gungun mutane dauke da makamai ne suka kai hari kan ginin al'adun gargajiya na kasar Saudiyya da ke kasar Sudan, tare da lalata kayan aiki da na'urorin daukar hoto, da sace wasu daga cikin cibiyar.

An bayyana a cikin wannan sanarwa cewa: Ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai kan ginin ofishin raya al'adu a birnin Khartoum tare da neman a mutunta hedkwatar diflomasiyya da kuma hukunta wadanda suka kai wadannan hare-hare.

Har ila yau, ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta jaddada bukatar Riyadh na dakatar da ci gaba da ruruwar wutar rikicin soji tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a Sudan, domin kawo karshen tashin hankalin da kuma kare jami'an diflomasiyya, jama'a da fararen hula na Sudan.

 

 

4138408

 

captcha