IQNA

Za A Gudanar da taro na hudu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi a kasar Saudiyya

17:05 - June 01, 2022
Lambar Labari: 3487370
Tehran (IQNA) Saudiyya za ta karbi bakuncin taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na hudu a ranakun 5 da 6 ga watan Yunin 2022.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin na yanar gizo na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya bayar da rahoton cewa, taron na hudu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi zai samu halartar mahalarta daga nahiyoyi da kasashe daban-daban, da kuma wakilan majalisar dinkin duniya, da kungiyar agaji ta Red Cross, Red Crescent. , cibiyoyin bincike na musamman da ƙwararrun yanki da na duniya.

Makasudin gudanar da wannan taro dai shi ne karfafa matsayin kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da yin musanyar fasahohi masu inganci a shiyya-shiyya da na duniya, da hana tashe-tashen hankula, da warware matsaloli, da kuma karfafa aikin diflomasiyya.

4061159

 

 

 

captcha