IQNA

Sayyid Nasrullah: Isra'ila Ta Kama Hanyar Rugujewa Sakamakon Tsayin Dakan Falastinawa

16:36 - April 12, 2022
Lambar Labari: 3487158
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Abin da ke faruwa a Palastinu a yau yana da bangarori da dama kan batun fada da gwamnatin sahyoniyawan da kuma makomar wannan gwamnatin ta mamaya.

Yayin da yake jinjinawa tsayin dakan al'ummar Palastinu, a wani jawabinsa a daren jiya Sayyid Nasrullah ya ce: Tare da dukkan girmamawa, muna yaba wa da jarumtar al'ummar Palastinu, domin samar da rayuwa mai daraja da 'yantar da tsarkakakkun wurare na al'umma."

Yayin da yake magana ga gwamnatin sahyoniyawan Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa: Idan kun yi tunanin cewa al’ummar Falastinu sun yanke kauna, to kun kasance a cikin rudani, domin wannan al’umma mai tsayin daka ba za ta taba mika wuya da kuma saryar da hakkinta ba.

Ya ci gaba da jawabin nasa da yin kira ga dukkanin al'ummar musulmin duniya da su shiga cikin ayyukan tunawa da ranar Qudus ta duniya a ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da mamayar da Isra'ila ta yi wa kasar Labanon a watan Afrilun shekarar 1996, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Tsayawa kan dugadugi da juriya shi ne babban sirrin nasarar al’ummar Lebanon a yakinsu da Isra’ila a 1996, da sauran yakoki da suka yi da ita bayan hakan.

A karshe Sayyid Nasrallah ya yi maraba da shirin tsagaita bude wuta a kasar Yaman tare da bayyana fatan cewa wannan tsagaita wutar za ta bude kofar tattaunawa ta siyasa ta kuma zama mafarin kawo karshen yakin, tare da kawo karshen killacewar da masu yaki da al’ummar Yemen suke yi wa kasar.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4048702

captcha