IQNA

Nasrullah: Dole Ne Hizbullah Ta Kasance A Majalisar Dokokin Lebanon Domin Kare Gwagwarmayarta

18:30 - March 17, 2022
Lambar Labari: 3487065
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, dole ne Hizbullah ta kasance a cikin majalisar dokokin Lebanon domin kare manufofinta na gwagwarmaya.

Babban sakataren kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa wajibi ne kungiyar ta shiga dukkan harkokin siyasa na kasar Lebanon, kama daga majalisar dokoki da kuma gwamnatin kasar, ba wai don karfafa kungiyar kawai ba, sai dai tabbatar da cewa kawayen kungiyar sun sami nasara a zabubbukansu gaba daya, don a tafi tare da su.

Jaridar Annashr ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a wani taron da ya yi da manya-manyan jami’an kungiyar a birnin Beirut a safiyar yau Laraba.

Sayyid Nasarallah ya ce muna bukatar dukkan kawayemmu su sami nasara a zaben 15 ga watan Mayu mai zuwa don nasaransu ita ce nasararmu. Ya kuma kara da cewa zaben majalisar dokokin kasar Lebanon mai zuwa shi ne zabe mafi muhimmanci da kuma hatsari a tarihin siyasar kasar, ganin irin yadda makiyan kasar suka sa kungiyar da kawayenta a gaba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4043342

captcha