IQNA

Kungiyoyin Gwagwarmaya A Falastinu Sun Taya Murna Kan Kwato Jirgin Ruwanta Da Amurka Ta Yi Fashinsa

21:11 - November 04, 2021
Lambar Labari: 3486514
Tehran (IQNA) Ofishin yada labarai na kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa ya taya sojojin ruwa na IRGC murnar kwato jirgin ruwan Iran da Amurka ta yi fashinsa a cikin teku.

Shafin yada labarai na Al-ahad ya ce, Kwamitin ya bayyana cewa,  a yau dakarun kare juyi sun yi amfani da wannan mataki na karfi wajen yakar sojojin ruwan Amurka, inda ya ce makiya al'ummar musulmi kawai suna fahimtar harshen arangama da karfi ne kawai ba lalama ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau tana kafa wani sabon tsari na fuskantar Amurka mai taken "A'a ga girman kai da wuce gona da iri a yankin gabas ta tsakiya.

Kwamitin ya kammala da cewa za a kawar da kwadayin Amurka da kasashen yammacin duniya a kan  dukiyar al'ummar musulmi, da take hakkinsu ta hanyar dagewar da Iran ta yi da kuma nuna jarunta wajen dakile wadannan makirce-makircen da kuma ci gaba da tsayin daka.

 

4010452

 

captcha