IQNA

Sayyid Nasrullah: Mu Yi Amfani Da Kafofin Yada Labarai Da Na Sadarwa Wajen Kare Musulunci Daga Harin Makiya

16:44 - August 13, 2021
Lambar Labari: 3486197
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, dole ne mu yi amfani da kafofin yada labarai da na sadarwa wajen kare addinin musulunci daga harin makiya.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a jawabinsa na raya dararen Muharram, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, dole ne mu yi amfani da kafofin yada labarai da na sadarwa wajen kare addinin musulunci daga harin makiya a fagen yakin sadarwa. 

Sayyid Nasrullah ba dukkanin yaki ne ake yi makamai ba, akwai yaki ta hanyoyi daban-daban, yakin da aka fi yi a halin yanzu shi ne yakin kafofin yada labarai da na sadarwa, inda a nan take za a iya murguda gaskiya a mayar da ita karya, ko mayar da karya ta zama gaskiya, kuma a yayata hakan har mutane da dama su gamsu ta kafofin sadarwa.

Ya ce wannan yaki a halin yanzu har a kan Imam Hussain (AS) da alayen manzon Allah (SAW) ana aiwatar shi ta kafofin sadarwa, inda wasu suke amfani da wadannan kafofi wajen kokarin juya gaskiyar abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) a ranar Ashura, har da kokarin dora laifi a kan Imam Hussain (AS) da ahlul bait na manzon Allah (SAW).

A kan haka ya ce ya zama wajibi musulmi su mike wajen kokarin kare addinin musulunci daga irin wadanann hare-hare da ake kai kansa ta hanyoyin sadarwa da na yada labarai.

 

3990183

 

captcha