A cikin wani bayani da ya fitar, kwamitin kare hakkokin musulmi a kasar Ingila ya bukaci da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harka Islamiyya a Najeriya, tare da mai dakinsa malama Zinat Ibrahim.
Wannan kira yana zuwa ne a lokacin da kotu ke sauraren shari'ar sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa malama Zinat Ibrahim a Kaduna.
Babbar kotun jihar Kaduna a Najeriya, ta sanya ranar da 28 ga Yuli a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar da ake wa Sheikh Ibrahim Zakzaky da maidakinsa.
A zaman na ranar Alhamis, dukkan lauyoyin masu gabatar da kara da wadanda ake kara sun yi wa kotu bayani.
Babban lauya ga Malam El-Zakzaky, Femi Falana SAN, wanda ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan dage zaman, ya bukaci Kotun da ta yanke hukunci a kan shari'ar wadanda yake karewa.
Tun a shekara ta 2015 ne dai ake tsare da malamin, da maidakinsa bayan farmakin da sojoji suka kaddamar a Zariya.