IQNA

Yaki Da Ta’addani Manufa Ce Guda Da Ta Hada Kasashen Syria Da Iran

23:50 - December 08, 2020
Lambar Labari: 3485442
Tehran (IQNA) shugaba Hassan Rauhani na Iran ya jaddada matsayin kasarsa na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Syria wajen yaki da ta’addanci.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mikdad da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Iran, ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar ta Iran.

Shugaba Rauhani ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da ci gaba da kara karfafa alaka tsakanin Syria da Iran a fagage daban-daban da suke yin aiki tare, da hakan ya hada da batun yaki da ta’addanci.

Rauhani ya ce tsayin da jajurcewar al’ummar Syria gwamnatinsu da da sojojinsu da sauran al’ummar kasa, shi ne babban sirrin samu nasararsu a kan makircin da aka kullawa kasar da nufin rusa ta, saboda matsayarta ta kin amincewa da mika wuya ga manufofin kasashe masu girman kai da ‘yan korensu na yankin.

Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa kawayen Syria ba za su bar ta ita kadai ba a duk lokain da take bukatarsu, kamar yadda suka kasance tare da ita a fagen yaki da ta’addanci da ‘yan ta’adda a cikin kasarta.

Kasashen na Siriya da Iran, sun sha alwashin karfafa alakar dake tsakaninsu, ta fuskar tattalin arziki da kuma sauran bangarori na syasa da ilimi noma da sauransu.

Wannan yana kunshe ne a sanarwar bayan taron da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar, yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Siriya a Tehran.

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawwad Zarif, ya ce yana da kyau a rika samun irin wannan tattaunawa lokaci zuwa lokaci tsakani Iran da Siriya dama wasu kasashe.

A nashi bangare ministan harkokin wajen kasar ta Siriya, Faisal Mekdad, godewa Iran ya yi game da irin goyan bayan da take baiwa kasarsa kan yaki da ta’addanci da tsatsauran ra’ayi.

A daya bangaren ya kuma ya isar da sakon ta’aziyya na shugaban Bashar Al-Assad da al’ummar Siriya, game da kisan babban masanin nukiliyar kasar ta Iran Mohsen Fakhrizadeh.

Haka na kuma ya kuma kalubalanci ayyukan Amurka a yankin wanda a cewarsa su ne ke kara rura wutar rikici a yankin.

Shi ma a nasa bangaren babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran ya bayyana cewa, Syria da Iran za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori.

 

3939818

 

 

captcha