IQNA

An Bukaci A Kare Hakkokin Mabiya Mazhabar Shi’a A Najeriya

22:46 - September 09, 2020
Lambar Labari: 3485166
Tehran (IQNA) Gamayyar wasu kungiyoyin farar hula daga kasar Switzerland da kuma Najeriya, sun bukaci a kare hakkokin mabiya mazhabar shi’a a Najeriya.

A cikin wani rahoto da gamayar kungiyoyin farar hula ta The coalition of Civil Society Organisations, da ke da mazauni a kasar Switzerland, da kuma wata kungiya ta kare hakkokin musulmi a Najeriya mai suna CEDRA suka fitar, sun bayyana cewa dole ne mahukunta su kare hakkokin mabiya mazhabar shi’a a Najeriya, suna yin ishara da magoya bayan Harka Islamiyya a kasar.

Bayanin na hadin gwiwar kungiyoyin ya bayyana hakkokin bil adama da kare ‘yancinsu na yin addinin da suka dama a matsayinsu na ‘yan kasa a matsayin halastaccen lamari a dokokin Najeriya, wanda suka yi ishara da ayar doka ta 33 a fasali na hudu a cikin kundin tsarin mulkin 1999.

A daya bangaren bayanin an yi ishara da farmakin da sojoji suka kaddamar a kan gidan jagoran Harka Islamiyya a Najeriya sheikh Ibrahim Zakzaky a karshen shekara ta 2015 a Zaria, wanda hakan ya yi sanadiyyar kisan daruruwan magoya bayansa a wurin, tare da kama shi tare da mai dakinsa da kuma daruruwan magoya bayansa, tare da yin tir da hakan, da kuma kiran mahukunta da su kawo karshen tsare shi.

3921870

 

 

 

 

 

captcha