IQNA

An Bukaci Gudanar Da Bincike Kan Take Hakkokin Bil-Adama A Yamen

23:53 - September 12, 2017
Lambar Labari: 3481887
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kwamitin kolin Kare Hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gudanar da bincike kan take hakkokin bil-Adama a yakin wuce gona da iri da aka kaddamar kan kasar Yamen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a jawabin da shugaban kwamitin Kolin Kare Hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Zaid bin Ra'ad Alhusaini ya gabatar a birnin Geneva a jiya Litinin ya fayyace cewa: Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da kashe fararen hula musamman mata da kananan yara fiye da dubu biyar a hare-haren da jiragen saman kawancen Saudiyya suke kai wa kan sassa daban daban na kasar Yamen, don haka akwai bukatar gudanar da binciken kasa da kasa kan lamarin.

Ra'ad Alhusaini ya kara da cewa: Hare-haren wuce gona da iri da ake kaddamarwa kan kasar Yamen tare da rusa kasar yana dauke da mummunar sakamako kan dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don haka akwai bukatar gudanar da binciken kasa da kasa domin gano hakikanin irin barnar da ake tafkawa a cikin kasar.

3641074


captcha