IQNA

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Saki Malam Zakzaky

22:37 - December 02, 2016
Lambar Labari: 3480994
Bangaren kasa da kasa, kotun tarayya a Najeriya ta bayar da umarni ga mahukuntan kasar kan sakin sheikh Ibrahim Zakzaky.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Press TV cewa, a yau juma'a Kotun ta ce a Sakin Sheikh El-Zakzaky Tare Mai Dakinsa, Sannan kuma a biya su wasu kudade.

Kotun koli ta tarayya da ke birnin Abuja,ya yanke hukuncin a saki Sheikh Ibrahim Yakubu el-zakzaky tare da mai dakinsa, da kuma biyansu diyyata kudaden.

Hukuncin Kotun wacce mai shari'a Gabriel Koluwale ya jagoranta, ya yi watsi da dalilin na jami'an tsaro na ciki su ka bijiro da shi na cewa suna ci gaba da tsare malam din ne domin bashi kariya, idan ya ce; Ba a baiwa mutum kariya ba tare da sonsa ba.

Har ila yau, alkalin ya ce dole ne gwamnatin tarayya ta baiwa Sheikh El-zakzaky diyyata kudin da su ka kai naira miliyan ashirin da biyar mai dakinsa ma Malama Zeenata kwatankwacin haka.

Wani sashe na bayanin yanke hukuncin ya kunshi cewa a bai wa malam Zakzaky wurin da zai zauna, a cikin birnin Zaria, ko kuma duk inda ya ke so a cikin Najeriya.

Wa'adin sakin Sheikh Zakzaky din dai kotun ta ayyana shi ne kwanaki 45.

3550309


captcha