IQNA

An Hukunta Mutumin Da Ya Wulakanta Wata Musulma Mai Hijabi

22:46 - October 19, 2016
Lambar Labari: 3480865
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a kasar Amurka ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan kaso da kuma daurin talala na watanni biyu.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Independent cewa, Gill Parcker Pine ya fuskanci hukuncin daurin shekara guda a gidan kaso da kuma daurin talala na watanni biyu a gida, da kuma biyan tara ta pan 815 sakamakon cin zarafin wata musulma.

Gilla cikin watan Disamban shekara ta 2015 ce ya ci zarafin wata musulmi da take sanye da hijabi, a lokacin da yake tafiya acikin jirgi da ke zuwa jahar New Mexico daga Caroline ta arewa, inda a cikin jirgi ya ga wata musulm sanye da hijabi, y ace dole ne ta cire shi, domin a kasar Amurka ne, bayan da ta ki saurarensa, ya cire mat hijabi da karfin tsiya.

Dimon Martins shi ne babban alkalin Amurka, ya kuma bayyana cewa duk wanda yake tsammanin cewa zai ci zarafin wani tare da tsora shi saboda akidarsa ta addini, to ya kwana da sanin zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi a kotu.

Mutumin dai ya bayyana nadamarsa, inda y ace ya ziyarci daya daga cikin masallatai, kuma ya gane cewa ya kuren fahimta a kan musulmi, saboda haka yana bayar da hakuri ga wannan mata.

3539170


captcha