IQNA

Hukunci Mai Tsanani Kan Magoya Bayan Ikhwan 418

23:35 - August 19, 2016
Lambar Labari: 3480726
Bangaren kasa da kasa, wata kotun kasar masar ta yanke hukunci mai tsanani kan magoya bayan kungiyar Ikhwan muslimin su 418 a kasar Masar.
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Press TV cewa, kotun ta kasar Masar ta yanke hukunci kan mutane 350 da suke a gabanta har shekaru 25 a gidan kaso, wasu 68 kuma shekaru 2 zuwa 10 1 gidan kaso.

Kotun ta yankewa mutane 350 daga cikin kungiyar Ikhwan hukuncin daurin rai da rai. Labarin ya kara da cewa, kotun wacce ta zauna a birnin Asyun, banda wadan nan mutane kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu zuwa gomaga wasu muatne 68.

Kotun ta tabbatar da laifin tada hankali a dai dai lokacinda jami'an tsaro suke kokarin tarwatsa wadanda suka yi zaman Dirshen a masallacin Rabi'a bayan juyin mulkin da sojoji suka yiwa gwamnatin Muhammad Mursi a shekara ta 2013.

Har'ila yau wasu kuma ana zargnsu na lalata wurare jami'an tsaro da kuma kayakin gwamnati.Mutane 249 daga cikin wannan adadin dai basa hannu jami'an tsaron kasar aka yanke masu wannan hukuncin.

A watan da ya gabata ne ma'aikatar shari'ar kasar mika takardun karar ga kotun ta Soje, duk kuwa da cewa dai wannan ab shi ne karon farko da kotunan gwamnatin Masar suke yanke irin wannan hukunci kan magoya bayan kungiyar ba, domin kuwa yanzu haka akwai wadanda aka yankewa daurin rai da rai, wasu kuma hukuncin kisa.

3523799

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna masar magoya bayan hukunci wasu shekaru ikhwan
captcha