IQNA

Sabbin bayanai na lalata ofishin ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma

17:44 - May 05, 2023
Lambar Labari: 3489091
Tehran (IQNA) Bayan lalata ofishin Ilhan Omar, wakiliya Musulma a Majalisar Dokokin Amurka, hukumomi sun zargi wanda ake zargi da kona masallatai a Minneapolis da hannu a wannan barna.

A rahoton da jaridar al-Quds al-Arabi ta bayar, wakilan ofishin mai gabatar da kara sun sanar da cewa, hukumomin jihar Minnesota sun zargi wanda ake zargi da haddasa gobara a wasu masallatai biyu a birnin Minneapolis da bata ofishin Ilhan Omar, 'yar majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyar Democrat.

A cewar sanarwar lauyan gundumar Minnesota, 'yan sandan Blue Earth sun kama Jackie Ram Little mai shekaru 36 a ranar Lahadin da ta gabata, kuma a cewar Brian O'Hara, babban jami'in 'yan sandan birnin, wadannan ayyukan wani yunkuri ne na haifar da ta'addanci a cikin Amurka ta hanyar cutar da  Al'ummar musulmi.

Bayan gobarar da aka yi a ranakun 23 da 24 ga Afrilu da kuma sammacin kama Jackie Ram, yanzu haka yana fuskantar tuhuma kan laifin lalata ofis na wakiliya a majalisar dokoki.

A cewar kotun, Jackie Ram ya bayyana a cikin ikirarin nasa cewa ya barnata kayan ofishin din wani dan majalisa kuma duk da cewa ba a ambaci sunan wannan dan majalisar ba, amma Ilhan Omar ta bayyana cewa ofishinta ne kadai aka lalata.

Tun da farko an kai hari a wasu masallatai biyu a birnin Minneapolis na Amurka.

Kona masallacin ya zo ne makonni kadan bayan da Minneapolis ya zama birni na farko a Amurka da ya ba da damar yin kiran sallah da lasifikan masallaci sau biyar a kowace rana.

Rahoton Majalisar Musulmin Amurka (CAIR) mai taken "Rahoton Kare Hakkokin Bil'adama na shekarar 2018" ya yi nuni da faruwar al'amura 144 na keta alfarma a kan masallatai a shekarar 2017, 57 daga cikinsu laifukan nuna kyama ne.

 

4138616

 

 

captcha