IQNA

Rahoton Jaridar Times Kan kisan Musulmi A Afirka Ta Tsakiya

17:06 - September 06, 2017
Lambar Labari: 3481870
Bangaren kasa da kasa, jaridar Times ta bayar da rahoto dangane da halin musulmin kasar Afirka ta tsakiya suke ciki inda suke fuskantar kisan kiyashi daga kiristoci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumaria News cewa, jaridar Times ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, msuulmin jamhuriyar Afirka ta tsakiya suna cikin mawuyacin hali na fuskantar kisan kyashi.

Wasu daga cikin 'yan bindiga kiristoci sun kai hari kan wani malamin addinin kirista saboda ya bayar da mafaka ga wasu daga cikin musulmi da ake neman kashwa wadanda adadinsu ya kai kimanin dubu biyu.

Jaridar ta Times ta kara da cewa, wannan babban malamin addinin kirista ya kasance a sahun gaba wajen yin kira da a daina kasha musulmi, tare da yin kira da a basu kariya, kuma a taimaka ma wadanda suka samu raunuka.

Wani alakali a musulmi ya bayyana abin da musulmi suke fuskanta na kisan kiyashi da abin da yake faruwa a Mayanmar, inda ake yi wa musulmi kisan kare dangi da nufin ganin bayansu baki daya.

A cikin rahoton nata jaridar Times ta ce, idan ba a dauki matakin takawa 'yan ta'adda daga cikin kiristoc da ke kasha musulmi ba, to lamarin zai dauki wani salo wanda ba zai yi wa kowa dadi ba.

3638736


captcha