IQNA

Kwafin Kur'ani Da Aka Bayar Ga Hubbaren Imam Hussain (AS) Daga Najeriya

20:33 - March 11, 2017
Lambar Labari: 3481303
Bangaren kasa da kasa, masu kula da littafan hubbaren Imam Hussain (AS) sun bayyana cewa an kyautata kwafin kur'ani da wani dan Najeriya ya bayar kyauta ga wannan hubbare mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, Manaf Tamimi shugaban bangaren kula da littafai na hubbare yana cewa, sun gudanar da wani akin a musamman a kan kur'anin da wani dan najeriya ya bayar kyuata ga hubbaren Imam Hussain (AS)

Ya ci gaba da cewa, daga cikin da aka gudanar, har da yin ma kur'anin makangai na fata mai kwarin gaske, wadda aka kawata ta, da kuma yin amfani da wasu sanadarai a kan takardun ta yadda ba za su rududduge ba, domin hakan zai bayar da dama a adana wannan kwafin kur'ani mai matukar kima da aka rubuta da hannu a Najeriya.

Tamimi ya ce wannan kwafin kur'ani ya shiga cikin littafai da kayan tarihi na wannan hubbare wanda za a ajiye shi a dakin kayan tarihi na hubbaren Imam Hussain (AS).

Abin tuni a nan dai shi ne, tawagar da ke gudanar da ayykan kyautata kwafin littafai da ake adanawa a wannan hubbare, tana da alaka ne da jami'ar birnin Kufah.

3582833
captcha