Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Ahmed Fahmy, kakakin fadar shugaban kasar Masar, ya sanar da cewa, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ziyarci masallacin Annabi bayan kammala taron kasashen Larabawa a birnin Jeddah.
Hotunan da kafafen yada labaran Saudiyya da na Masar suka wallafa na wannan taron sun nuna yadda shugaban kasar Masar ke addu'a a masallacin.
Shugaban kasar Masar ya yi Umrah a lokacin da ya isa kasar Saudiyya.