IQNA

Hizbullah: Ya Kamata Bikin Murnar Haihuwar Annabi Isa (AS) Ya Zama Lokaci Na Hada Kan Al’umma

18:16 - December 27, 2021
Lambar Labari: 3486737
Tehran (IQNA) Hizbullah ta yi fatan cewa tarukan tunawa da haihuwar Annabi  Isa (AS) za su karfafa hadin kai a tsakanin al’umma musamman ma dai mabiya addinai da aka saukar daga sama.

Shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah a taron malaman addini na kasar Lebanon ya bayyana fatan cewa tarukan tunawa da haihuwar Annabi  Isa (AS) za su karfafa hadin kai a tsakanin al’umma musamman ma dai mabiya addinai da aka saukar daga sama.

Sayyid Hashim Safi al-Din shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ya taya daukacin al'ummar kasar Labanon murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (AS) da kuma jaddada cewa: Annabi Isa Almasihu kalmar Allah ce mai kira zuwa ga hadin kai ba rarraba ba.

Safi  al-Din ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na malaman kasar Lebanon da kungiyar Hizbullah ta shirya a garin Tirfalsia da ke kudancin kasar mai taken "Kalubalen da ake ciki a halin yanzu da makoma a  gaba", wanda ya samu halartar jami'an kungiyar Hizbullah da gungun malamai na sunna da shi’a hard a wasu kiristoci.

Babban kusan na Hizbullah ya kammala da cewa: Idan har wasu daga cikin ‘yan kasar Labanon da ke samun  goyon bayan kasashen waje suka so raunana karfin kasar Lebanon da tsayin daka da al'ummarta da sojojinta suka yi, to muna gaya musu cewa kun sake yin kuskure kamar yadda kuka yi a baya, Amma bambancin wannan lokacin shine ba za ku sami wani sakamako ba, kuma hakarku ba za ta cimma ruwa ba.

 

 

4023823

 

 

 

captcha