IQNA

Nasrullah: Kasar Lebanon Ba Za Ta Taba Shiga Yakin Basasa Ba Kamar Wasu Suke Fata

20:42 - August 04, 2021
Lambar Labari: 3486170
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa kasar Lebanon ba za ta taba shiga cikin yakin basasa ba.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kokarin makiyar kungiyar wajen tunzurata ta shiga cikin yakin cikin gida ba zai kai ko ina ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Nasarallah yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da wasu shuwagabannin kungiyar bayan kissan Ali Shibli wani dan kungiyar a garin Jiyeh a lokacin da yake halattar wani bikin aure a makon da ya gabata.

Jami’an tsaron kasar Lebanon sun gano wanda ya bindige Shibli har lahira, mai suna Ahmad Zahir Ghosn daga dangin larabawan Ghosn da ke a yankin.

Ahmad ya na zargin cewa kungiyar Hizbullah ce ta kasha dan’uwansa Hassan a cikin watan Augustan shekara ta 2020 da ta gabata.

Sayyid Nasarallah ya musanta zargin cewa yayan kungiyar ne suka kashe Hassan, ya kuma bukaci jami’an tsaron kasar Lebanon su gudanar da bincike don tabbatar da adalci.

 

3988481

 

 

captcha