IQNA

An Bayyana Tsare-Tsaren gasar Kur'ani Ta Duniya A Masar

22:04 - August 02, 2021
Lambar Labari: 3486161
Tehran IQNA) an bayyana tsare-tsaren gasar kur'ani ta duniya da za a gudanara kasar Masar.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar Ali Mukhtar Juma'a ya bayyana cewa, an fitar da tsare-tsaren gasar kur'ani ta duniya da za a gudanara kasar.

Ya ce wannan shi ne karo na ashirin da takwas da za a gudanar da wannan gasa, wadda za a bayar da kyautar fam miliyan daya na kasar Masar ga wanda yafi nuna kwazo, wato kimanin dalar Amurka dubu 63 da da 618..

mMinistan ya ce gasar za ta tabo bangarori daban-daban, da hakan ya hada da hardar kur'ani mai tsarki, sai kuma bangaren tilawa, da kuma sauran bangarori da suka hada da sanin hukunce-hukuncen karatun kur'ani ko kuma Tajwidi.

Akwai sauran bangarori da suka hada da sanin wasu ilmomi da suke cikin kur'ani da kuma ma'anar kalmomin larabci na balaga da suke ciki.

Haka nan kuma shekarun wadanda za su shiga gasar zai zama kasa ad shekaru talatin ne, kamar yadda kuma za a bayar da dama ga masu bukatu na musamman amma kasar Masar domin su shiga cikin gasar.

 

3987890

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bukatu na musamman
captcha