IQNA

Wani Dan Wasan Sudan Ya Janye Daga Wasannin Olympics Japan Saboda Bayahuden Isra’ila

20:06 - July 26, 2021
Lambar Labari: 3486141
Tehran (IQNA) Dan wasan Judo na kasar Sudan ya janye daga gasar Olympics ta Japan domin kada ya hadu da dan wasan Judo na Isra’ila a karawarsa ta gaba.

Jaridar Ra'ayul yaum sun ce, Muhammad Abdulrasul Dan wasan Judo na kasar Sudan ya janye daga gasar Olympics ta Japan da ke gudana a halin yanzu, domin kada ya hadu da dan wasan Judo na Isra’ila a karawarsa ta gaba.

Dan wasan na Sudan wanda ya kai zagaye na uku a gasar Judu a wasannain Olympics na Japan 2020, amma karawa ta gaba zai hadu da bayahuden Isra’ila, wanda hakan yasa ya yanke shawarar cewa ya fice daga gasar baki daya.

Kwanaki biyu da suka gabata dan wasan kasar Aljeriya Fathi Nurain ya sanar da irin wannan mataki na janyewa daga wasan baki daya, domin kada ya hadu da bayahuden Isr’aila a wasansa.

Dukkanin ‘yan wasan biyu na Sudan da Aljeriya sun bayyana cewa sun yi hakan ne domin kara tabbatar da goyon bayansu ga al’ummar Falastinu marasa kariya, da kuma nuna rashin amincewarsu da zaluncin da Falastinawa suke fuskanta daga gwamnatin yahudawan Isra’ila.

 

 

3986486

 

 

captcha