A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya harhada, a jiya ne gudanar ad tarukan idin Ghadira jami’ar Almustafa a kasar Afirka ta kudu tare da halartar shugaban reshen jami’ara kasar Murteza Agha mohammadi, da kuma wasu daga cikin malamai gami da dalibai.
Bayanin y ace wannan taro yana daga cikin tarukan da aka saba gudanarwa a kowace shekara, wanda jami’ar take daukar nauyin gudanar da shi.
A wanann karon dai bayan malamai da dalibai, an kuma gayyaci wasu daga cikin masana da malaman addini daga bangarori daban-daban, inda wasu suka gabatar da jawabai a wurin, wasu sun gabatar da jawabai ta hanyar yanar gizo.