IQNA

UNRWA Ta Bayyana Damuwa Kan Halin ‘Yan gudun Hijira Falastinawa A Lebanon

22:54 - August 09, 2020
Lambar Labari: 3485068
Tehran (IQNA) hukumar kula da Falastinawa ta majalisar dinkin duniya ta UNRWA ta nuna damuwa kan halin da Falastinawa ‘yan gudun hijira za su iya shiga a Lebanon.

A cikin wani bayani da ta fitar a yau, hukumar kula da Falastinawa ta majalisar dinkin duniya ta UNRWA ta nuna damuwa kan halin da Falastinawa ‘yan gudun hijira za su iya shiga a Lebanon bayan abin da ya faru, wanda ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

A cikin bayanin, hkumar ta bayyana cewa akwai dubban Falastinawa wadanda suna cikin halin bukatar taimako tun kafin Lebanon ta shiga cikin halin da ta samu kanta, wanda hakan ko shakka babu zai tasiri a kan Falastinawa da suke gudun hijira a wannan kasa.

Hukumar ta bukaci tallafin aggawa daga kasashen duniya domin taimaka falastinawa ‘yan gudun hijira da suke rayuwa a cikin kasar Lebanon, bayan da Isra’ila ta kore su daga Falastinu.

Yanzu haka dai akawi kasashen duniya ad suka fara aki tallafi zuwa Lebanon.

 

3915534

 

captcha