IQNA

‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Mutane 10 A Chadi

21:19 - August 02, 2020
Lambar Labari: 3485046
Tehran (IQNA) ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kashe fararen hula 10 a yammacin kasar Chadi.

Shafin yada labarai na alyaum ya bayar da rahoton cewa, a jiya Asabar ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hari a cikin lardin Albuhaira da ke yammacin kasar Chadi, inda suka kashe fararen hula akalla goma.

Rahoton ya ce bayan kisan mutane , ‘yan ta’addan kuma sun tafi da wasu fararen hula 7 da suka hada har da mata biyu wadanda babu labarin makomarsu.

A cikin shekarun da kungiyar Boko Haram ta kwashe tana kaddamar da hare-hare ya zuwa yanzu ta kashe dubban mutanen a cikin kasashen Najeriya, Kamaru, Nijar da kuma Chadi da sunan jihadi.

Sakamakon barazanar tsaro da wadannan kasashe suke fuskanta daga wadannan ‘yan ta’adda ne shugabannin kasashe suka kafa runduna ta yaki da wannan kungiya.

 

3914081

 

 

 

captcha