IQNA

Mahmud Abbas Da Putin Sun Tattauna Kan Batun Falastinu

23:55 - July 09, 2020
1
Lambar Labari: 3484969
Tehran (IQNA) Fadar Kremilin ta sanar da cewa Vladimir Putin ya gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho tare da shugaban Falastinawa Mahmud Abbas.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a jiya Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tuntubu Mahmud Abbas ta wayar tarho, inda suka tattauna kan halin da ake ciki kan batutuwa da suka shafi wanzar da zaman lafiya a tsakanin Falastinawa da Isra’ila.

A yayin zantawar Putin ya jaddada wa Abu Mazin cewa, Rasha tana nan kan bakanta, na ganin cewa an warware matsalar Falastinawa da Isra’ila bisa dokoki na kasa da kasa, tare da yin adalci a cikin lamarin.

A ganawar da ta gudana tsakanin Putin da Abbas a cikin watan Janairun da ya gabata a garin Bait Laham ma Putin ya jaddada wannan matsaya, inda ya ce Rasha tana goyon bayan gwamnatin Falastinu, tare da kare hakkokinta kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shata.

Haka nan kuma Putin ya sheda wa Abbas cewa Rasha a shirye take ta bayar da dukkanin taimakon da ya kamata ga al’ummar Falastinu wajen yaki da cutar corona a cikin wannan yanayi da ake ciki.

Mahmud Abbas ya yi jinjina wa matsayar da kasar ta Rasha take dauka dagane da sha’anin Falastinu da kuma kare hakkokin Falastinawa a matsayi na kasa da kasa.

 

 

3909536

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
AMINU ABUBAKAR
1
1
Assalamu alaikum warahmatullah wabakatuh
dan Allah inason a bani amsar wadannan tambayoyi:-
shin wadannan rikice-rikice na yankin palastinu da isra'ila minene asalinsa???

me ya jawo rikicin yemen???

shin wai da gaske ne saudiyya ce ke renon duk wata kungiya ta ta'addanci a gabas ta tsakiya???

da gaske Qasim sulaimani jagoran 'yan ta'addan amurjawa ne a gabas ta tsakiya???
captcha