IQNA

Musawi Ya Yi Tir Da Hare-Hare Kan Yemen

19:43 - July 30, 2019
Lambar Labari: 3483895
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, ya yi tir da mummunan harin da kawancen da Saudiyya take jagoranta ya kai a garin Sa’aada wanda ya yi sanadin kashe fararen hula masu yawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya mika sakon jajantawa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su a cikin kasuwar garin na Sa’aada.

Abbas Musawi ya ci gaba da cewa; bayan shekaru hudu na yaki, Saudiyya ba ta cimma wani abu ba, illa barna, tare da kashe kananan yara da mata domin rufe kashin da su ka sha.

Tun a shekarar dubu biyu da sha biyar ne dai Saudiyya ta fara kai wa kasar Yemen hari, da zummar mayar da gwmanatin shugaba Abdurabbuh maimurabus, sai dai ya zuwa yanzu hakan ba ta samu ba.

Fiye da mutane dubu casa'in da daya ne kawancen da Saudiyyar take jagoranta ya kashe a cikin kasar Yamen, tare da jikkata wasu dubun dubata.

 

3830978

 

captcha