IQNA

Ana Barazana ga ‘yar majalisar Amurka musulma saboda sukar zaluncin gwamnatin Isra’ila  

15:53 - October 22, 2023
Lambar Labari: 3490018
Washington (IQNA) Wakiliyar majalisar wakilan Amurka ta bayyana cewa an yi mata barazana saboda sukar da take yi kan ayyukan gwamnatin sahyoniyawan a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, 

Jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyar Democrat a jihar Minnesota ta bayyana cewa, tana fuskantar barazana mai hadari, wadda ka iya shafar iyalanta.

Ilhan Omar wadda daya ce daga cikin mata musulmi a majalisar dokokin Amurka, ta ce saboda sukar da ta yi kan yadda gwamnatin sahyoniyawan ke yi wa Falasdinawan kisan kiyashi, an yi mata barazana a lokuta daban-daban, har ma ga iyalanta.

Wakiliyar 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dokokin Amurka daga jihar Minnesota ta yi magana a cikin wata sanarwa game da karuwar kalaman kyamar Musulunci da kuma barazanar da take fuskanta, gami da barazanar da ake yi wa iyalanta.

Ilhan Omar ta ce, ita da sauran Musulman Amurka sun fuskanci mummunan tasiri a yakin da ake yi na bata suna da kyamar musulmi, sakamakon yakin da ake yi tsakanin gwamnatin sahyoniya da Hamas.

Dangane da haka, ta yi ishara da kalaman da wasu 'yan majalisar masu ra'ayin mazan jiya suka yi da suka kwatanta ta da sauran wakilan da ke goyon bayan Gaza a matsayin magoya bayan 'yan ta'adda.

Ilhan Omar ta bayyana cewa kawo yanzu wasu mutane biyu da ba a san ko su waye ba sun yi mata barazanar kisa sannan ta ce ta damu matuka da lafiyar ‘ya’yanta saboda wadannan kalamai.

 

4176910

 

captcha