IQNA

Sojoji Da Dakarun Kare Juyi Za Su Gaba Da Aiki Tare Domin Kare Kasarsu

23:33 - April 18, 2019
Lambar Labari: 3483556
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, dakarun kare juyin juy halin musulunci da sojojin Iran za su ci gaba da yin aiki tare da wargaza shirin Amurka a kan Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran Juiyn juya halin musulunci na Iran Aya. Sayyid Ali Khamenei ya ce; Rawar da sojojin Iran suka taka wajen fada da kungiyar yanta’adda ta Daesh ba ta da tamka.

A jiya Laraba ne dai, da take jajiberin ranar Soja ta kasa a nan Iran, jagoran juyin musuluncin ya gana da kwamandojin sojajoji da na dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar a gidansa.

Jagoran ya kara da cewa bai san abinda zai faru a yankin gabas ta tsakiya ba, da ace dakarun kare juyin musulunci da sojojin kasar Iran ba su yaki Daesh ba

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma yi kira ga sojojin kasar da su kara riko da addini fiye da kowane lokaci. Har’ila yau ya kuma jinjinawa sojoji da dakarun kare juyin musulunci a kan rawar da su ka taka wajen taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta rusta da su a nan Iran a cikin yan makonni da suka gabata.

Daga karshe jagoran ya jaddada muhimmancin ci gaba da samun hadin kai a tsakanin sojoji da kuma dakarun kare juyin juya halin musuluncin kasar. Yau Alhamis ce, wato 18 ga watan afrilu take ranar sojoji a nan kasar Iran.

An gudanar da farati na ranar sojoji a mafi yawan manyan biranan kasar, inda aka jadda goyon bayan baya ga dakarun kare juyin juya halin musulunci , dangane da matakin da Amurka ta dauka na saka su cikin jerin ‘yan ta’adda.

3804716

 

 

 

 

 

 

captcha