Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ‘Yan majalisa 204 ne daga jimillar ‘yan majalisa 256 suka amince da bayyana rundunar tsakiya ta sojojin Amurka da Santicom da dukkanin bangarorin da suke karkashinta a matsayin ‘yan ta’adda. Bugu da kari kudurin ya kuma bayyana cewa duk wani taimakon da za a iya wa wannan rundunarna kudi, ko na bayanan sirri ko kayan aiki, daidai yake da taimakawa ayyukan ta’addanci.
Har ila yau, kudurin ya kira yi gwmanatin jamhuriyar musulunci ta Iran da ta dauki matakan da take ganin sun dace wajen fuskantar ayyukan ta’addancin Amurka da suke a matsayin barazana ga manufofin jamhuriyar musulunci ta Iran.
A makon da ya shude ne dai Amurka ta bakin shugaban kasar Donad Trump ta bayyana dakarun kare juyin musulunci na Iran a matsayin ‘yan ta’adda.