IQNA

Amurka Ba Ta Da Hurumin Yin Magana Kan Kare Hakkokin 'Yan Adam

23:35 - November 25, 2018
Lambar Labari: 3483148
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi, ya mayar wa Amurka da martani dangane da batun kare hakkin bil adam a Iran da kuma ayyukan ta'addanci.

kamfanin dillancin labaran iqna, A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya, Bahram Qasei ya bayyana cewa; Amurka ba ta da hakkin da za ta yi magana a kan kare hakkin bil adama a wata kasa, domin kuwa hatta batun hakkokin 'yan adam a  wurin Amurka batu ne na kasuwanci.

Qasemi ya ce baya ga take hakkokin 'yan adam da cin zarafin mutane saboda dalilai na launin fata ko abin da ya yi kama da haka da ake yi a Amurka, a lokaci guda kuma kasar za ta iya zargin wasu kasashe da keta hurumin 'yan adam, a daidai lokacin da take yin gum da bakinta a kan  wasu masu zubar da jinin bil adam, saboda makudan biliyoyin daloli da take karba daga gare su.

Bahram Qasemi ya ce shin ba abin kunya ne ga Amurka ta fito tana zargin wasu kasashe da take hakkin bil adama ba? a  daidai lokacin da take taimaka ma kashe da ke kashe dubban mata da kanan yara a kasashen yankin gabas ta tsakiya? Ya ce abin da yake faruwa a Yemen ya isa ya kara tabbatar da irin wannan salo na siyasar siyasar munafunci. 

3766776

 

captcha