IQNA

Rashid Ganushi: Ba Dora Ma Mutane Muslunci Da Karfin Tsiya

20:52 - October 21, 2017
Lambar Labari: 3482025
Bangaren kasa da kasa, Rashid Ganushi shugaban kungiyar Nahda a kasar Tunisia ya bayyana cewa jihadi ba shi da ma'ana idan ya zama manufarsa shi ne tilasta mutane su shiga musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin Anatoli cewa, Rashid Ganushi shugaban kungiyar Nahda a kasar Tunisia,a lokacin da yake gabatar da jawabi a birnin Istanbul na Turkiya, ya bayyana cewa jihadi ba shi da ma'ana idan ya zama manufarsa shi ne tilasta mutane su shiga musulunci ko da ba su yi niyyar hakan ba.

Ganishi ya ce a kowane lokaci muslunci yana girmama ra'ayin da akidun mutane, kuma yana kiransu ne zuwa ga koyarwara ta hanyar hikima ba ta hanyar yina mfani da karfi ko tilasci ba.

Ya kara da cewa, jihadi a muslunci yana sharudda da kaidoji, kuma jihadi yana zuwa ne domin kariyar kai daga makiya da suka afka ma musulmi ko kuma suka cutar da su, ko kuma suke yin barazana akansu.

Ya ce musulmunci shi ne hakikanin demukradiyya domin kuwa ya baiwa dana dam dama domin ya zabi abin da yake so ba tare da tilasci ba, tare da koyar da dabiu na kyautatawa ga kowa, kamar yadda manzon Allah ya koyar da musulmia aikace, inda kyawawan dabiunsa sun sanya wasu musulunta.

Daga karshe Ganushi ya yi kira da a mayar da hankali wajen aikata ayyukan alkhari na taimakon raunana da wadanda ake zalunta kamar al'ummar Rohingya da kuma Palastine.

3655020


captcha